Tsohon Dan Wasan Flying Eagles, Bello Mohammed ya koma sana’arsa gadi.
Bello Mohammed Ya buga wasa a Flying Eagles ta Najeriya a tsakanin shekarar 1999-2000, inda ake yi masa lakabi da ‘Bello Sudan’ saboda kuzarinsa da karfinsa.
Dan wasan wanda a kodayaushe a shirye yake ya ba da ransa ga kasarsa, majiyoyi sun tabbatar da cewa yanzu shi jami’in gadi ne a wata cibiya a Abuja.
Bello ya buga wasa a El-Kanemi Warriors, Yobe Dessert Stars, da Zamfara United.
YA buga wasa a Najeriya, tareda Taurarin yan wasa irin su: Isa Hudu, marigayi Justice Christopher, Christian Obodo, Kelechi Okoye, Olaniyi Olayinka, Austin Ejide, Aniekan Enyeama, Dele Aiyenugba, Ajibade Omolade, Onyebuchi Chukwumah da dai sauransu.
Turawa Abokai