Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi zargin cewa shugaban hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, AbdulRasheed Bawa, na zargin sa ne, saboda ya ki ba shi cin hancin dala miliyan 200,000.
A ranar Alhamis, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa ta na binciken gwamna Matawalle bisa zargin karkatar da kudaden jihar Zamfara har sama da Naira biliyan 70.
A wata hira da BBC Hausa a ranar Juma’a, gwamna Matawalle ya musanta zargin satar kudaden jihar.
“Bincike abu ne me kyau, kuma ba na inkarin shi. Amma kada ya zama abun zabi ne, ya kamata binciken ya zama akan kowa, ba ya tsaya kawai a iya gwamnoni ba, Shin Gwamnoni ne kawai ke da damar samun kudaden gwamnati, ai Ministoci suna nan; su ma ya gayyace su domin a yi binciken mana,” inji Matawalle.
Ya kuma bukaci Mista Bawa da ya mika kansa domin bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa.
“Ina kuma kalubalantar shi (Bawa) da ya gabatar wa duniya takardun da ya ce yana da su akan mu (gwamnoni). Sannan kuma ya kamata ya mika kansa domin a bincike shi domin akwai tarin tuhume-tuhumen akansa.
“Akwai sama da mutane 200 da suka shirye su ba da shaida a kansa kuma su gaya wa duniya cewa da hannayensa dumu-dumu a cikin cin hanci da rashawa.
“Ya san abin da ke tsakaninmu, ya nemi wata alfarma a gare ni, ni kuma na ki, don haka ya zabi ya bata min suna, amma ban damu ba.
“Duk zarge-zargen da ake yi mani, karairayi ne. Ya nemi cin hancin dala miliyan biyu a wurina, ni kuma na ki ba shi, ina da shaiduna.
Matawalle ya ce a wata ganawar da suka yi da shi, shugaban EFCCn ya zarge shi da rashin ziyartar ofishin sa kamar yadda sauran gwamnoni ke yi.
Ko da BBC ta tuntuba don jin ta bakinsa, Bawa ya ce duk da mutum Tara ya ke bai cika goma ba amma ya kalubalanci Matawalle da ya fallasa duk wani zargin zamba da ake yi masa.