CITAD ta gano wani ƙauye a Kano da ke cikin gagarumar matsalar rayuwa

144

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato Centre for Information Technology and Development (CITAD), ta gano wani kauye a yankin ƙaramar Albasu a jihar Kano da al’ummar wannan kauye su ke fuskantar matsaloli daban-daban.

Cibiyar ta CITAD ta rawaito cewa mutanen ƙauyen Yarimari – Hungu da ke cikin ƙaramar hukumar Albasu ta jihar Kano sun ce fiye da shekara ashirin suka shafe a cikin matsalar ƙarancin ruwan sha tare da rashin makarantar Firamare da kuma ɗakin shan magani.

Gurin da al’ummar ƙauyen Yarimari ke ɗiban ruwan sha da amfanin yau da kullum

Ƙauyen na Yarimari – Hungu mai nisan kilomita fiye 60 daga birnin Kano yana tsakanin ƙananan hukumomin Garko da Sumaila, kuma al’ummar ƙauyen na fama da matsalar ruwan sha tsawon lokaci.

Yadda Dabbobi da Mutane su ke shan ruwa a guri guda

Al’ummar ƙauyen sun bayyanawa CITAD cewa da zarar ruwan damina ya ɗauke to tun daga nan sun fara fargaba kan halin da za su tsinci kan su kan batun ruwan da za su yi amfani da shi na yau da kullum.

Alhaji Muhammad na ɗaya daga cikin Dattawan wannan ƙauye na Yarimari ya bayyana cewa “Muna fuskantar kalubale daban-daban da su ka haɗa da matsalar ruwan sha da rashin makarantar Firamare da kuma rashin asibiti”

“Saboda matsalar rashin ruwan shan da mu ke fuskanta a wannan gari yaranmu ba sa samun damar zuwa makaranta akan lokaci wasu lokutan ma hakura su ke yi da makarantar gaba ɗaya”

“Gurin da mu ke samun ruwa wani rami ne da aka samar da shi tun lokacin Abubakar Rimi yana gwamnan Kano. Guri ne da aka ɗebi ƙasar da aka yi aikin hanya daga nan ne ya zama gurin diban ruwa ga al’ummar wannan ƙauye” In ji Alhaji Muhammadu

Hakazalika, al’ummar Yarimari sun shaidawa CITAD cewa gwamnati ba ta gina musu makarantar Firamare a wannan gari ba, sai dai su ne su ka haɗu su ka gina makarantar Firamare domin ƴaƴansu su samu ilimi.

Makarantar Firamaren a ƙauyen Yarimari

Babannan Adamu, shi ne shugaban matasan garin Yarimari – Hungu ya bayyana cewa “Muna da yara masu yawa a wannan gari da mu ke son su yi ilimi. Kuma gwamnati ta taɓa yi mana alƙawarin samar mana da makaranta da kuma ruwan sha. Amma kullum sai sa rana ake yi daga ƙarshe da mu ka fahimci abin ba zai samu ba, sai mu ka taru da kanmu mu ka gina wannan makaranta”

Allon da ake koyawa yara karatu
Cikin Ajin da yara su ke ɗaukar darasi

Garin dai na Yarimari – Hungu yana da yawan mutanen da su ka wuce 500, kuma baya ga matsalar ruwan sha da rashin makarantar Firamare, su na fuskantar matsalar rashin asibiti wanda hakan ya ke sanyawa mata su ke rasuwa a lokacin da haihuwa ta zo da tangarɗa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan