A ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayanin yadda gwamnatinsa ta kashe Dala Miliyan 322 da ta ƙwato daga iyalan marigayi Janar Sani Abacha.
A wata sanarwa da Babban Mataimakin Shugaban Ƙasa kan Kafafen Watsa Labarai, Garba Shehu ya fitar, Shugaban ya ce an yi amfani da kuɗin ne wajen shirin rarraba Naira Duba Biyar da ake yi duk wata ga gidajen talakawa sama da dubu ɗari uku ƙarƙashin Shirin Rage Raɗaɗi.
Ya ƙara da cewa kashe kuɗin ya yi daidai da Yarjejeniyar Fahimtar Juna, MoU da aka cimma tsakanin gwamnatocin Najeriya da gwamnatin Switzerland a matsayin wani sharaɗin sakin kuɗin.
A cewar Mista Shehu, a wani ɓangaren Yarjejeniyar Fahimtar Junar, MoU, Bankin Duniya ne yake lura da yadda ake raba kuɗin, ya ce Bankin ya ƙaro ƙarin tallafi don taimakawa shirin raba kuɗin da ake ci gaba da yi.