Yi wa yara kanana fyade a Majami’un Amurka na daduwa a kowacce rana

121

Rahotanni da ake kai wa jami’an tsaro game da yi wa yara kanana fyade a Cocinan Amurka na ci gaba da karuwa a kowacce rana.

Bayan da kamfanin dillancin labarai na Associated Press AP ya fitar da rahoton cewa, a Majami’iun katolika na Amurka ana yi wa daruruwan yara kanana fyade, a yanzu an buga sunayen dubunnan Malaman Coci dake yi wa yara kanana fyade a kasar.

Binciken da AP ya gudanar ya ce, bayan binciken sheklaru 2 da mai gabatar da kara na Pensilvania Josh Shapiro ya yi kan zargin fyade ga yara kanana ya gano Majami’ar katolika dake Pensylvania ta boye fyaden da aka gano Malaman Cocinansu sun yi wa yara kanana kuma an aikata hakan sama da sau dubu.

An sanar da cewa, daga watan Agustan bara zuwa yau an fitar da sunayen kusan Malaman Coci 50 da suka yi fyade ga yara kanana kuma a yankuna da dama za a yi hakan.

Haka zalika ana bincikar wasu majamisu a yankuna da jihohin Amurka b,sa zargin aikata fyaden.

An fara zargin yin fyade a wuraren bautar Kiristoci a Amurka tun a shekarar 1910. Kuma kaso 60 na Malaman cocin da ake zargi ba sa raye a yau wanda hakan yake sanya wa a ajje shari’ar da ake yi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan