Dakataccen Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa ya koma APC

296

Dakataccen mataimakin shugaban jam’iyyar hamayya ta PDP na Arewa, Babayo Gamawa ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
A ranar Litinin ne jam’iyyar ta PDP ta dakatar da Mista Gamawa sakamakon zargin sa da wasarairai da aiki da kuma yi wa jam’iyya zagon kasa.
Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan, wanda ya sanar da dakatarwar, ya ce Babban Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar PDPn ne ya dakatar da Mista Gamawa.
Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ne ya sanar da canza shekar ta Mista Gamawa ranar Talata.
Mista Adesina ya wallafa hotunan Mista Gamawa da Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar lokacin da su ka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa.
“Shugaba Buhari ya karbi sababbin shiga jam’iyyar APC, tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP, Sanata Babayo Garba Gamawa da Onorabul Kaulaha Aliyu bisa rakiyar Gwamnan Jihar Bauchi a Fadar Gwamnati ranar 8 ga watan Janairu, 2019”, Mista Adesina ya wallafa haka a shafinsa na Facebook.
Ranar 5 ga watan Janairu ne jam’iyyar PDP ta yi taron ganawa, inda ta yi bitar korafin da aka yi akan Mista Gamawa na zargin wasarairai da aiki da kuma ayyukan yi wa jam’iyya zagon kasa.
Daga bisani ne kuma ta dakatar da shi daga jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkinta Sashi na 58 (1) ya tanada.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan