Home / Gwamnati / Siyasa Ta Raba Kawunan Fulani A Jihar Taraba
Gwamna Darius Dickson

Siyasa Ta Raba Kawunan Fulani A Jihar Taraba

An samu rarrabuwar kawuna a hadakar ƙungiyoyin makiyaya a jihar Taraba, inda a karon farko wasu kungiyoyin makiyaya suka ce sun yafewa gwamnatin jihar tare da bayyana goyon bayansu ga jam’iyar PDP a zabe mai zuwa, yayin da wasu ƙungiyoyin kuma ke cewa ba zata sabu ba.

Wannan ne karon farko tun bayan dambarwar kafa dokar hana kiwo da gwamnatin jihar Taraban ta kaddamar da gwamnan jihar Arc.Darius Dickson Isiyaku ke samun maslaha da hadakar kungiyoyin makiyaya, inda makiyayan suka mika mubaya’arsu ga gwamnatin PDP a jihar.

Mafindi Umaru Danburam dake zama shugaban kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah mai kula da jihohin arewa maso gabas da ya jagoranci kungiyoyin makiyayan zuwa gwamnatin jihar yace su sun yafe duk abubuwa da suka faru a baya.

A bangarensa kuma, gwamnan jihar Taraban Akitet Darius Dickson Isiyaku ya karyata zargin cewa gwamnatinsa na nunawa musu wariya.

Sai dai kuma yayin da wannan ke faruwa wasu kungiyoyin Fulani sun ce bada yawunsu aka je gidan gwamnatin ba, un kuma ce jam’iyar APC zasu bi. Sahabi Mahmud shine shugaban kungiyar miyetti Allah a jihar

Gwamna Darius Dickson
ya jagoranci wani taron manema labarai inda suka bayyana matsayinsu da cewa su APC zasu yi ba wata jam’iya ba.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Shugabannin Addini Da Na Siyasa Na Ƙoƙarin Kifar Da Gwamnatina— Buhari

Fadar Shugaban Najeriya ta ce wasu ‘yan Najeriya marasa kishin ƙasa na ƙoƙarin haɗa kai …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *