Darakta Janar na yakin neman zaben Atiku ya koma APC

158

Darakta Janar na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a Arewa Maso Gabas, Sanata Sa’idu Umar Kumo ya koma jam’iyyar APC.

Mataimakin Shugaba Muhammadu Buhari akan sababbin kafafen watsa labarai, Ahmad Bashir shi ya sanar da canza shekar ta Mista Kumo a shafinsa na Twitter.

Mista Bashir ya ce canza shekar Mista Kumo alama ce dake nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi nasara a zaben shugaban kasa na watan Fabrairu.

“Sanata Sa’idu Umar Kumo daga Gombe kuma Darakta Janar na Kwamitin Yakin Neman Zabe na Atiku/PDP a Arewa Maso Gabas ya bar jam’iyyar PDP ya shiga jirgi mai tafiya #NextLevel. Hudu a tara da hudu ta PMB ta tabbata in Allah Ya yarda”, Mista Bashir ya rubuta haka a shafinsa na Twitter.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan