Taƙaitaccen Tarihin Sabon Muƙaddashin Babban Sifeton Ƴan Sanda

210

An haifi sabon Mukaddashin Sifeton ‘Yan Sanda na Kasa, Mohammed Abubakar Adamu ranar 17 ga watan Satumba, 1961 a Lafiya dake jihar Nasarawa inda ya yi ilimin firmarensa a can. Daga bisani ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya inda ya samu shaidar karatun digiri a Ilimin Labarin Kasa a shekarar 1983.

A shekara ta 2010, ya yi digiri na biyu a Tsarin Dokokin Manyan Laifuka na Kasa da Kasa a Jami’ar Portsmouth dake Ingila. A shekara ta 2018, Jami’ar Godfrey Okoye dake Inugu ta ba Mukaddashin Sifeton ‘Yan Sanda Mohammed Digirin Digirgir na Girmamawa a Ilimin Dangantakar Kasashe sakamakon jajircewarsa akan aiki.

Mukaddashin Sifeton ‘Yan Sanda Adamu ya fara aikin dan sanda ne a shekarar 1986, lokacin da ya fara aiki da Rundunar ‘Yan Sanda a matsayin Mataimakin Sufurtandan ‘Yan Sanda, ya kuma samu horo ne a Kwalejin ‘Yan Sanda dake Ikeja.

A shekarunsa aikinsa na farko, ya yi aiki a matsayin Jami’in Kula da Manyan Laifuka kuma Jami’in Gudanarwa a Ofishin ‘Yan Sanda dake Mgbidi dake Mgbidi a jihar Imo, ya kuma yi aiki a matsayin O/C na Bincike Gaba Daya a Shelkwatar ‘Yan Sanda, Shiyya ta Shida dake Kalaba, ya yi aiki a matsayin jami’i mai bincike tare da kama masu aikata muggan laifuka a Sashin Binciken Manyan Laifuka da Bayanan Sirri na Rundunar ‘Yan Sanda dake unguwar Alagbon, a Ikoyi, jihar Legas. Ya yi aiki da kungiyoyi manya-manya inda aka daga likafarsa ya zama Babban Jami’in Bincike Tare da Kama Masu Aikata Muggan Laifuka.

Tsakanin 2007 zuwa 2010, Mohammed ya yi aiki a matsayin Daraktan Aikin Kiyaye Zaman Lafiya da Bada Horo a Shelkwatar Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa dake Abuja, bayan nan an kai shi jihar Ikiti inda ya yi aiki a matsayin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da Gudanarwa a Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ikitin.

Tsakanin 2012 zuwa 2013, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda kuma Shugaban Sashin Binciken Manyan Laifuka a Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna. An kai shi jihar Inugu a matsayin Kwamishinan ‘Yan Sanda daga shekarar 2013 zuwa 2015, ya kuma zama Mataimakin Babban Sifeton ‘Yan Sanda na Kasa a Shiyya ta Biyar ta Rundunar ‘Yan Sanda dake Birnin Benin daga 2016 zuwa 2017.

Mohammed dan sanda ne da ake ganin yana da dumbin kwarewa a aikin dan sanda, kuma yana da gogewa a aikin na dan sanda a wurin da yake da al’umomi mabanbanta. Daga 1997 zuwa 2002, an daga likafarsa daga Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya zuwa Babbar Sakatariyar Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa da Kasa, INTERPOL, dake Lyon a Faransa a matsayin Kwararren Jami’i akan laifukan da suka shafi yi wa tattalin arziki zagon kasa a Sashin Binciken laifukan da suka shafi yi tattalin arzikin zagon kasa na INTERPOL din.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan