Zazzabin Cutar Lassa Ya Sa Ke Kuno Kai

170

Ma’aikatar lafiya ta ƙasa ta ce an samu asarar rayukan mutane 16 sakamakon sake ɓullar zazzabin Lassa a wannan wata na Janairu shekarar 2019. A watan Mayu na shekarar 2018 ne hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce anyi nasarar shawo kan Cutar Lassa waddda bera ke yadawa a ƙasar nan.

A cewar WHO a makwanno 6 da suka gabata ana samun raguwar cutar yayinda a yanzu ake da mutane kalilan da ke fama da cutar a kasar wadda ta yi fama da barkewar cutar a baya.

Sashen yaƙi da cututuka masu sauƙin yaɗuwa na ma’ikatar lafiya, ya ce a jimilce mutane 172 ne aka kebe bisa zaton cewa sun kamu da zazzabin a wannan wata, inda aka tabbatar da cewa 60 daga cikinsu na dauke da cutar ce.

Kawo yanzu dai sashen kiwon lafiya na ci gaba da tanttance hanyoyin shawo kan wannan matsalla tareda taimakon hukumar lafiya ta Duniya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan