Tarihin Shugabannin Ƴan sandan Najeriya tun daga Farko zuwa Yau (2)

359

Ga cigaban Tarihin shugabannin hukumar ƴan sanda ta Najeriya kamar yadda muka fara kawo muku a cikin rahotanmu na ɗaya.
Ga masu son karanta rubutun farko sai su danna ƙasa
Tarihin Shugabannin Ƴan sandan Najeriya tun daga Farko zuwa Yau (1)
ALHAJI MUSILIU ADEOLA KUNBI SMITH:

Shi ne shugaban Rundunar Yansanda na goma. An haife shi a ranar 17 ga watan April shekarar 1946 a garin Olowogbowo, jihar Lagos. Yayi karatu a makatar Ansarud-deen collage, Isolo a jihar Lagos da kuma Jami’ar tarayya da ke jihar Lagos.

Ya shiga rundunar Yansanda a shekarar 1972. Daga nan ya rike mukamai da dama har ta kaishi ga shugabancin rundunar. Bayan yayi ritaya daga rundunar, ya rike mukamin chairman board of directors na skye bank a shekarar 2016. A shekarar 2017, gwamnan jihar lagos na lokacin Babatunde Fashola ya nada shi shugaban state security council.

MUSTAFA ADEBAYO BALOGUN:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na Sha Daya. An haife shi a ranar 8 ga watan August shekarar 1947 a Ila Oragun, jihar Osun.

Ya kammala karatunsa a jami’ar lagos a shekarar 1972 kuma ya samu shiga rundunar Yansanda ta kasa a shekarar 1973. Ya rike mukamai da dama tare da samun karin girma har zuwa lokacin da aka nadashi shugabancin rundunar Yansanda ta kasa, a shekarar 2002.
Ya gudanar da tsare-tsare na cigaban rundunar. Ya sauka daga wannan mukami a shekarar 2005.

SUNDAY GABRIEL EHINDARO:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na Sha Biyu. Ya samu mukamin shugabantar rundunar Yansanda a shekarar 2005 zuwa shekarar 2007. Shi dan asalin garin Oyin-Akoko ne dake jihar Ondo amma an haife shi a garin Jos.

Yayi karatu a makarantun Gboluji Grammar school, Ondo da Jami’ar Ibadan.
Bayan kammala karatunsa, ya fara aikin koyarwa a garin Abeokuta, jihar Ogun. A lokacin da yake rike da rundunar, yayi kokari wajen ganin an samu daidaito tsakanin jinsin maza da mata a cikin rundunar. Yayi yaki da cin-hanci da rashawa a cikin al’umma da kuma cikin rundunar ta yansanda.

MIKE MBAMA OKIRO:

Shi ne shugaban Rundunar Yansanda na Sha Uku. An haife shi a ranar 24 ga watan July a shekarar 1949, a garin Oguta jihar Imo. Amma ya kasance dan asalin jihar River daga karamar hukumar Egbema.

Ya samu digirinsa na farko da na biyu a jami’ar Ibadan. Sannan kuma ya samu shaidar karatu na LLB da LLM daga jami’ar Jos. Ya samu shiga rundunar yansanda a shekarar 1977. Ya rike mukai da dama a bangarori daban-daban har zuwa lokacin da aka nada shi shugabancin rundunar yasanda ta kasa a shekarar 2007.

Daga cikin nasarorin da ya samu sun har da; ya gabatar tsarin yin rijistar layukan waya domin samu bayanai akan masu yin amfani da layukan waya, ya kawo tsarin Amnesty international domin taimakawa yan tawayen Niger delta, ya gabatar da tsarin yin amfani da CCTV camera a bankuna domin karfafa tsaro, ya kaddamar da bincike akan ci hanci da rashawa mussaman akan wasu kudi da aka yi almundahanarsu a bangaren danyan mai da kimarsu ta kai dala miliyan 190.

Mr Okiro yayi ritaya a watan August shekarar 2009. A ranar 8 ga watan Mayu a shekarar 2013 tsohon shigaban kasa GoodLuck Jonathan ya zabi Mike Okiro domin zama shugaba na police service commission wanda majalisar dattawata tabbatar da shi. Baya ga haka, Mike ya kasance mutum mai san rubuce rubuce kuma ya kaddamar da littafai da suka shafi fannoni daban-daban na rayuwa.

OGBONNA OKECHUKWU ONOVO:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na hudu. An haifi a ranar 7 ga watan Febuary shekara ta 1953 a karamar hukumar Nkanu dake jihar Enugu. Kamala digirin sa na farko a shekarar 1976 daga jami’ar Nigeria dake Nsukka.

Ya shiga rundunar Yansanda na kasa a shekarar 1977 kuma yayi ta samu Karin girma har ya kai matsayin mataimakin shugaban hukumar Yansanda ta kasa. Ya dade yana rike da wannnan mukami inda yai aiki a karkashin shugabanni hukumar guda uku da suka hadar da Tafa Balogun, da Sunday Ehindaro da Mike Okiro.

Daga bisani aka nada shi shugabancin hukumar Yansanda na kasa a shekarar 2009 zuwa shekarar 2010. A shekarun 1998 zuwa 2000, ya rike mukamin chairman na National Drug Law Enforcement Agency. Ya kawo tsare-tsare tare da yaki da yan kungiyar Boko Haram a farkon kafuwarsu.

HAFIZU RINGIM:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na Sha biyar. An haife shi a ranar 1 ga watan April a jihar Jigawa. Ya samu damar zama shugaban rundunar yansanda ta kasa a shekarar 2010 zuwa shekarar 2012.

MUHAMMAD DUKKO ABUBAKAR:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na Sha shida. An haife shi a ranar 5 ga watan May, shekara ta 1960 a garin Gusau jihar Zamfara. Ya samu mukamin shugabancin rundunar yansanda a shekarar 2012 zuwa shekarar 2014.

SULEIMAN ABBA:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na Sha bakwai. An haife shi a ranar 22 ga watan march shekara ta 1959 a garin Gwaram jihar Jigawa. Ya kamala karatun digirinsa na farko daga jami’ar Jos. Ya shiga rundunar yansanda ta kasa a shekarar 1984, daga nan yayi ta samun karin girma har ya kai ga matsayin shugabantar wannan rundunar a watan August shekarar 2014 zuwa shekarar 2015.

SOLOMON EHIGIATOR ARASE:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na Sha takwas. An haife shi a ranar 21 ga watan June a shekarar 1956 a garin Oredo, jihar Edo. Ya kammala digirinsa na farko a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1980.
Ya samu shiga aikin rundunar Dansanda ta kasa, a ranar 1 ga watan December shekarar 1981. Ya sake yin digiri a fannin shari’a a jami’ar Benin, sannan ya kammala digirnsa na biyu a jami’ar legas.

An nada shi shugabancin rundunar yansanda ta kasa a watan April shekarar 2015 zuwa shekarar 2016. Ya rike mukamai da dama tare da samun lambobin yabo.

IBRAHIM KPOTOM IDRIS:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na Sha tara. An haife shi a ranar 15 ga watan Janairu shekarar 1959 a garin Kutigi, Jihar Niger.

Yayi karatun digirinsa na farko a fannin Noma daga jami”ar Ahmadu Belo dake Zaria, sannan ya kara wani digirin a fannin shari’a a jami’a Maiduguri. Ya samu shiga rundunar yansanda a shekarar 1984. Ya rike matakai da dama, daga bisani shugaban kasa mai ci shugaba Muhammad Buhari ya nada shi shugabancin rundunar yansanda ta kasa a ranar 21 ga watan March shekarar 2016 har zuwa ranar 15 ga watan January shekarar 2019.

MUHAMMAD ABUBAKAR ADAMU:

Shi ne shugaban Rundunar yansanda na Ashirin. An haife shi a ranar 17 ga wata September a shekarar 1961 a garin lafiya jihar Nasarawa. Ya kammala digirinsa na farko a jami”ar Ahmadu Bello dake Zaria, sannan kuma ya sake wani digirin a Portsmouth dake England. Ya shiga rundunar yansanda ta kasa a 1986.

Ya rike matakai daban-daban a rundunar, hakan yasa shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada shi Shugabancin rundunar yansanda ta kasa a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 2019.
Har yanzu shi yake rike da wannan matsayi amma na riko kafin tabbatar da shi ko kuma sauya shi.

Daga
Amina Hamisu Isa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan