Majalisar Wakilai ta amince da dokar mafi ƙarancin albashi

159
Zauren Majalisar Wakilai

A ranar Talata ne Majalisar Wakilai ta Kasa ta amince da dokar kara mafi karancin albashi zuwa Naira Dubu 30.

Dokar ta samu amincewa ne bayan da Majalisar ta duba rahoton kwamitinta na wucin gadi a yayin zaman nata.

A lokacin da ‘yan majalisun ke amincewa da dokar, sun yanke shawarar su bar mafi karancin albashin kamar yadda kwamitin nan mai ɓangarori uku ya amince.

Kwamitin dai tuni ya amince da Naira Dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da na jihohi.

Majalisar ta amince da dokar ne kimanin mako daya bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da dokar don yin nazari bayan da Majalisar Kasa ta amince da haka.

Amma Majalisar Kasar ta amince ne da Naira Dubu 27, yayinda Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kara wa ma’aikatanta mafi karancin albashin zuwa Naira Dubu 30.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan