Kashe-kashe: Gwamnatin jihar Zamfara ta buƙaci a yi azumin kwana uku

293
Gawarwakin mutanen da mahara suka kashe

Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga al’ummar jihar da su fara azumin kwana uku su kuma dukufa wajen yin addu’o’i don neman taimakon Allah bisa mahara, masu satar jama’a da masu aikata sauran laifuka da suka addadbi jihar.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu, Bello Dankande ne ya bayyana haka ga manema labarai a Gusau ranar Talata.

“Na tabbata duk kuna sane da kokarin da gwamnatin jiha da Gwamnatin Tarayya ke yi don kawo arshen aikata laifuka a jihar nan.

“Mun yi imani cewa azumin da addu’o’in za su sauƙaƙa samun taimakon Allah ga tsaro da nasarar jami’an tsaronmu, kuma za su kawo karshen wannan mummunan hali.

“Wannan azumi na kwanaki uku na nafila ne ga kowa da kowa saboda abin ya shafe kai tsaye ko ba kai tsaye ba.

“Muna kuma kira ga malamai da almajiransu da su yi saukar Ƙur’ani don neman taimakon Allah”, in ji Kwamishinan.

Ya kara da cewa dokar da ta hana sare itace da siyar da man fetur ba bisa ka’ida ba tana nan daram, yana mai nata cewa masu kunnen ƙashi za su fuskanci fushin hukuma.

“Hana sare itace da siyar da man fetur ba bisa ka’ida ba ya durkusar da aikace-aikacen maharan ya kuma shafi yadda ake kawo musu abinci, makamashi da sauransu”, in ji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya bada rahoton cewa a shekara ta 2018 ne gwamnatin jihar ta hana sare itace da siyar da man fetur ba bisa ƙa’ida ba.

“Wannan ya biyo bayan samun rahotanni dake cewa maharan na samun abinci, miyagun wayoyi, giya da sauran abubuwa da ake kawo musu ta hanyar masu sare itace da masu siyar da man fetur ba bisa ƙa’ida ba ga maharan”, a kalaman Kwamishinan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan