Darakta Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben PDP a jihar Gombe ya koma jam’iyyar APC.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Femi Adesina ya fitar ta ce Bala Bello Tinka wanda aka fi sani da Tinka Point ya hadu da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis da daddare a Fadar Gwamnati dake Abuja.
Misra Adesina ya ce a yayin wannan ganawa, Mista Tinka ya yi mubaya’a ga jam’iyyar APC, ya kuma lashi takobin tattara karfin siyasarsa waje daya don tabbatar da nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a wa’adi na biyu.
“Yayinda ya rage mako biyu kafin zaben shugaban kasa, canza shekar Alhaji Tinka ya yi wa jam’iyyar PDP babbar mahangurba a Gombe. Jam’iyyar PDP ce ke mulkin jihar a halin yanzu, kuma ta kasance tana mulkin tun shekara ta 2003.
“Shugaba Muhammadu Buhari zai je yakin neman zabe a jihar Gombe ranar Asabar, kuma ana sa ran Alhaji Tinka zai shiga jam’iyyar APC a hukumance da shi da wasu a lokacin yakin neman zaben”, in ji Mista Adesina.
Mista Tinka ya yi yunkurin samun tikitin takarar gwamna a jam’iyyar PDP amma bai yi nasara ba.
Mista Tinka dan kasuwa ne kuma babban dan kwangila ne a jihar. Shi ne mai kamfanin Tinka Point Limited, kamfanin da ya kafa a shekarar 1986, a lokacin ana kiran kamfanin Bala Tinka Enterprise.
Tuni kamfanin ya zama babban kamfanin gine-gine a kasar nan inda yake gina hanyoyi, zaizayar kasa da sauran ayyukan raya kasa ga Gwamnatin Tarayya da wasu gwamnatocin jihohi.
Mista Tinka babban abokin Gwamna Dankwambo ne, kuma ba a san me yasa ya koma jam’iyyar APC ba.
An samu rahotonni a watan Janairun 2018 dake cewa Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC ta tsare dan kasuwar sakamakon zargin sa da hannu a badakalar fitar da kudaden da PDP ta yi yakin neman zabe da su a 2015.