Katankatana: Wata Ƴar Fashi Mace ta shiga hannu a Legas

275

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Legas ta samu nasarar cafke wata mata da ta kware wajen yi wa direbobin tasi fashi.
A tare da wannan mata, an kama wasu maza guda biyu masu suna Zino Tochukwu Ude da Anumelechi Chris William.

Mutum biyun da aka kama, an same su dauke da muggan makamai kuma sun amsa laifin da ake zarginsu da shi.

A yanzu haka, jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu don kamo ragowar ‘yan kungiyar da suka gudu.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, Mista Imohimi Edgal ya bayyana cewa ba a bayyana sunan matar ba saboda tana taimaka masu wajen bankado asirin sauran abokan harkar nata.

Ya kara da cewa, sun samu rahoton aikin bata garin ta hannun wani direban tasi wanda suka yi wa fashi bayan da ya dauki ita wannan mata, daga bisani kuma ta bukaci da ya tsaya a wani wuri ta karbi kudi a hannun saurayinta.

Tsayawarsu ke da wuya sai ya ga maza mutum uku sun kewayesu su da makamai kuma suka kwace masa motar da wayoyinsa guda biyu da kuma kudi naira dubu N20,000.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan