INEC ita kadai ba za ta iya gudanar da zaben adalci ba- Okorocha

130
Gwamna Rochas Okorocha

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ita kadai ba za ta iya gudanar da zaben adalci ba.

Okorocha, wanda ya fadi haka a Owerri ya ce idan ana so zabukan su zama na adalci, dole sai hukumomin tsaro da kungiyoyin addini sun taka muhimmiyar rawa.

Mista Okorocha, wanda ya ce yana da kwarin gwiwa mai karfi game da Hukumar Zabe ya jaddada cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai lashe zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabrairu.

“Ina da kwarin gwiwa game da INEC, amma gaskiyar ita ce INEC ita kadai ba za ta iya tabbatar da zabuka na adalci ba. ‘Yan sanda, sojoji da dukkan hukumomin tsaro dole su shiga a yi da su. Kungiyoyin addini da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’uma dole su shiga.

“Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne kaifi daya kuma mai mutunci. Za a sake zaben sa, shi yasa muke mara masa baya. Ba za mu kyale su su yi zabukan magudi ba”, in ji Mista Okorocha.

Mista Okorocha ya ce zai ci gaba da aiki har ranar 29 ga watan Mayu, lokacin da zai mika mulki, duk da dai ya yi alfaharin cewa yunkurin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Sanata Hope Uzodinma da Sanata Osita Izunaso ba zai hana shi cin zabe zuwa Majalisar Dattijai ba.

Da yake kira da a mara wa dan takarar gwamna na jam’iyyar AA baya, Uche Nwosu, Mista Okorocha ya ce jihar za ta kasance a hannun mai amana idan Mista Nwosu ya zama gwamna.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan