Buhari ya gama faduwa zaben 2019- Obaze

170
Oseloka Obaze

Dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben gwamna da aka yi a jihar Anambra a shekara ta 2017 kuma Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku da Obi a jihar, Mista Oseloka Obaze ya ce tuni ‘yan Najeriya sun kori Shugaba Muhammadu Buhari daga gwamnati, ya ce zaben 2019 wata ka’ida ce kawai ta korar jam’iyyar APC da Shugaba Buhari.

Mista Obaze ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar yayin wani taron manema labarai a Awka, babban birnin jihar Anambra ranar Laraba.
A ta bakinsa, ‘yan Najeriya ba sa farin ciki da gwamnatin Buhari. Ya ce a halin yanzu ‘yan Najeriya fushi suke da Shugaba Muhammadu Buhari, kuma sakamakon haka, tuni fushin nasu ya kori Buhari.

Mista Obaze, wanda ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kasa cika ko kaso biyar cikin dari na alkawuran da ta yi wa ‘yan Najeriya a 2015, ya ce tuni ‘yan Najeriya sun ba gwamnatin sanarwa barin gidan gwamnati.

Ya ce idan ‘yan Najeriya suna so su shaki sabuwar iska, dole su kori jam’iyyar APC.

“Fiye da kaso 90 cikin 100 na ‘yan Najeriya ba sa farin ciki da gwamnatin nan. Tuni fushin ‘yan Najeriya ya kori Buhari a matsayin shugaban kasa.

“Gwamnatin ba ta aiwatar da kaso biyar cikin dari na alkawuran da ta yi wa ‘yan Najeriya ba a 2015.

“Akwai bukatar gwamnatin APC ta tafi don ta ba ‘yan Najeriya damar shakar iska. ‘Yan Najeriya sun gaji da su”, in ji Mista Obaze.

“Tuni ‘yan Najeriya sun ba gwamnatin sanarwar barin gidan gwamnati. Saboda haka, zaben 16 ga watan Fabrairu kawai wata ka’ida ce na korar gwamnatin.

“Ban ga dalilin da zai sa Buhari ba zai bari a yi zaben adalci ba. Ya kamata Buhari ya karbi faduwa karara da zai yi a zaben, ya tafi ba tare da kawo karin matsaloli ga Najeriya ba”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan