Kun san abokan da suka shafe shekaru fiye da 50 suna abota?

198

A wannan zamani da rikon amana da taimakon juna da aminci suka yi karanci a cikin al’aumma, sai ga shi an samu wasu aminai da abotarsu ta haura shekaru 55.

Wadannan abokanai masu suna Abraham Adedokun Olorode da Isaac Adetunji Adedeji, dukkansu ‘yan asalin jihar Oyo ne.

Mista Abraham ya girmi Mr Isaac da shekara 13.

Duk da sun fito daga jiha daya, amma ba su san juna ba sai bayan sun fara aiki a garin Ibadan bayan kowannen su ya yi aure.

Alakar da ke tsakanin mutanen biyu ta kullu ne a unguwar Alusekere dake Yankin Popo a garin Ibadan, a lokacin da Mista Isaac ya je wurin Mista Abraham domin ya yi wa maigidansa magana ya ba shi hayar filin da yake bayan shagon da yake sayar da siminti don ya rika sana’ar buga bulo.

“Ganin muna gudanar da sana’a iri daya, sai muka fara abota har ta kai ga mun shaku, shakuwa fiye da ‘yan uwan juna. Mun samu yarda da fahimtar juna fiye da wanda suka fito ciki dayya.

“Ganin cewa sana’armu tana alaka da juna, mu kanmu ba mu san lokacin da kasuwancinmu ya hade ya zama daya ba”, in ji Mista Abraham.

Ganin cewa kasuwancinsu ya zama daya, sai suka hada kai suke aiwatar da komai tare kama daga harkar saye da sayarwa wanda Mr Isaac ke tsaye a kai, cefanen gida da kula da Asusun Hadin Gwiwa na Banki wato Joint Account.

Ba a nan kadai alakar ta tsaya ba, hatta a fannin iyali nan ma tare suke yin komai. Suna zaune a gida daya, matan suna girki tare, rainon yara da, aikace-aikacen gida. Ba nan kadai ba hatta kasuwanci tare matan suke gudanarwa da sauran harkokin rayuwa kamar yadda mazan nasu ke yi.

Sukan raba aikin cikin gida inda mace daya za ta yi girki daya kuma ta lura da yara, don su samu su fita kasuwancinsu akan lokaci. Don haka ‘ya’yansu suka tashi tamkar ‘ya’yan mutum daya. Saboda wannan shakuwa, a wasu lokutan idan matan suka haihu a lokaci guda yi zaton ‘yan biyu ne.

Haka wadannan mutane suka ci gaba da rayuwa da dadi ba dadi har zuwa yanzu. Sun fuskanci kalubale da dama a rayuwarsu kama daga fadawa hannun ‘yan damfara, abinda ya yi sanadiyyar karayar arzikinsu, zuwa yi wa ‘ya’yansu tarbiyya da sauran su, amma wannan bai kawo wani tsaiko a abotar tasu ba. Suna alfahhari da wannan aminci nasu.

A yanzu da abotarsu ke neman cimma shekara 60, Mr Olorode ya ce abinda yasa amincinsu ya yi dogon zango shi ne gaskiya da rikon amana da wadatar zuci.

“Ba mu taba hangen abin da karfinmu ba. Ba mu bari san abin duniya ya shiga tsakaninmu ba, kuma mun yi riko da addini yadda ya kamata, hakan yasa rayuwarmu ta zama a saukake”, in ji Mista Olorode.

Daga karshe, ya ba matasa shawara da kada su yadda son abin duniya ko kaunar matansu ya shiga tsakanin abotarsu.

Sannan su ji tsoron Allah, su cire san kudi kuma su kaunaci juna, domin ta haka ne za su iya taimakon juna.

Mista Olorode da Mista Isaac sun kasance misali a zamanin yanzu da samun abota don Allah yake wahala.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan