An gudanar da Taron Kasa da Kasa kan Abinci Mai Lafiya

209

A ranar Talatar da ta gabata ne shugannin kasashen duniya suka gudanar Taron Kasa da Kasa Akan Samar da Abinci Mai Lafiya a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

Jigon taron na bana shi ne tabbatar da tsarin abinci mai lafiya yana gudana dai-dai da samarwa da kuma amfani da shi.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce abincin da ya gurbata da kwayoyin ‘Bacteria’, ‘Virus’, ‘Parasite’, ‘Toxins’ ko ‘Chemicals’ yana janyo cuta ga sama da mutum miliyan 600 da kashe mutum 420 a duniya kowacce shekara.

Cututtuka da suke da alaka da gurbataccen abinci sun zama karin nauyi ga tsarin kiwon lafiya tare da lalata tattalin arziki da kasuwanci da yawon shakatawa.

Taron ya samu halartar kasashen duniya 130, da wakilan masu saye da na masu sayarwa, da kungiyoyin al’umma da kungiyoyin sa kai.
Manufar wannan taro shi ne binciko hanyoyin da za a samar da abinci mai lafiya a yanzu da kuma nan gaba. Kungiyar Tarayyar Afrika, AU, Hukumar Kula da Abinci da Aikin Gona, FAO, Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya, WHO da Hukumar Kula da Kasuwanci ta Duniya WTO ne suka shirya taron.

Ana sa rana sake wani tarona ranar 23 zuwa 24 ga watan Afrilu a Geneva wanda zai mayar da hankali akan dangantakar abinci mai lafiya da kasuwanci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan