Har yanzu ba a karɓi Katinan Zaɓe 587,440 ba a Kano- INEC

131
Katinan Zaɓe na Din-din-din, PVCs

Kwamishinan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, na Jihar Kano, Farfesa Risqua Arab Shehu ya ce har yanzu akwai Katinan Zabe na Din-din-din, PVCs har 587, 440 da masu su ba su karba ba a jihar.

Mista Shehu ya bayyana haka ne ta bakin Jami’in Hudda da Jama’a na Hukumar, Alhaji Garba Lawal yayin wata ganawa da jaridar Vanguard ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa Katinan Zaben da ba a karba ba din suna daga cikin katinan mutane fiye da miliyan biyar da suka yi rijista a jihar, kuma an kawo karshen raba Katinan Zaben ranar Litinin da ta gabata.

Mista Shehu ya ce kawo yanzu, Hukumar ta kammala rarraba kayayyakin zabe da ba sa bukatar kulawa sosai zuwa ga dukkan kananan hukumomi 44 dake jihar.

Kwamishinan ya ce Hukumar ta kuma wallafa sunayen mutane masu kada kuri’a ta kuma tura su zuwa kananan hukumomi don rabawa zuwa rumfunan zabe a ranar zabe.

Ya yi nuni da cewa INEC ta dauki ma’aikatan wucin gadi tare da ba su horo da ba su gaza 51,000 ba a jihar Kano domin shirye-shiryen zaben ranar Asabar din.

Ya kara da cewa tuni aka tura ma’aikatan wucin gadin zuwa wuraren ayyukansu daban-daban, yana mai karawa da cewa an samar musu da matsugunai tare da biya musu kudaden sufuri don saukaka musu zirga-zirga a yayin zaben.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan