A safiyar yau asabar, hukumar zabe ta kasa ta bada sanarwan dage zabukan kasa inda aka kara sati guda akan ranakun da aka sanya na farko biyo bayan taron gaggawa da hukumar tayi a daren jiya a garin Abuja. Wannan hukunci da hukumar ta dauka yana so ya bar baya da kura bisa zarge-zargen da ya fito daga manyan jam’iyyun kasarnan akan matakin.
Ofishin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da matakin da hukumar zaben ta dauka. Mai magana da yawun ofishin yakin neman zaben shugaban kasan, Mr festus Keyamo ne ya fidda sanarwa a safiyar yau da ta zargi hukumar zabe da hada baki da jam’iyyar adawa ta PDP domin tafka magudin zabe.
Mr festus yace, ‘muna fatan INEC zata zama yarba ruwanmu a wannan harka ta zabe, domjn jita jitar da ake watsawa na nuna cewa an dage zaben ne da hadin bakin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wacce da ma bata shirya shiga zaben ba’.
A bangare guda kuma , jam’iyyar adawa ta PDP ta zargi jam’iyya mai mulki ta APC da sanya hukumar zabe dage zabukan kasa don samun damar tafka magudi. Shugaban jam’iyyar ta PDP Mr Uche Secondus ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau inda yace hakan ya nuna a fili cewa hukumar zabe ta gaza don haka shugaban ta ya kamata ya sauka cikin gaggawa.
Ya kara da cewa, jam’iyyar APC tayi amfani da duk wata dama da ta samu wurin ganin tayi magudi a zabukan kasarnan, kama daga kona ofisoshin hukamar da kayan aikin zabe dab da zabukan kasa zuwa hada rigingimu a garuruwan da PDP ke da magoya baya dayawa da kirkiran matsaloli da zai basu ikon samun nasara ko ta halin kaka. Ganin hakan su bata cimma ruwa ba, yasa suka fito da sabon salo ta hanyar daga zabukan kasa, hakan zai iya zama hadari ga damakaradiyya.
Daga karshe, Mr secondus yace, kashe-kashen da akayi a gatin kaduna wata hanya ce da APC tayi amfani da shi don tsorata mutane karsu fito zabe. Hakan wani yinkuri ne na cigaba dz mulkin kasa a lokacin da al’umma suka gaji da jam’iyyar ta APC.
Zuwa yanzu, ana jira aji bayanin da hukumar zabe ta kasa zata bayar na yin karin mako guda a dab da lokacin gudanar da zabukan kasa.