Saurari yadda wani babban Malami ya Caccaki Buhari babu tsoro a Kano (Audio)

247

Ba tun yau ba dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shan suka kan yadda yake tafiyar da wasu lamurran mulkinsa, musamman kan halin da talakawa na ka-kasa suka tsinci kansau a ciki na halin ni ‘ya su, inda har wasu da dama tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum ta gagare su.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari



Saurari jawabin Malamin

Yan siyasa da Malamai magada Annabawa da Sarakunan gargajiya da ma sauran mutanen gari na ganin baiken shugaban kasar bisa yadda ake tafiyar da wasu lammuran na mulki kamar hana shigo da abinci da Motoci ta kasa ta hanyar kulle iyakar kasar nan da ke arewacin Najeriya.

A cikin wannan rahoton na mun zakulo muku guda daga cikin irin wadannan kurafe-kurafe da wani babban shaihin Malami yayi a Kano Sheikh Lawan Abubakar Shu’aib Triumph a cikin wani zama da aka yi na karatu da niyyar korafin ya isa ga kunnuwan a kalla makusantan shugaban kasar koda bai samu kaiwa gare shi ba.

Wannan dai wani sashe ne na maganar Malamin ba duka ba, ga mai son jin gabaya sai ya nema don sauraren ragowar barin zaman karatun Malamin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan