Abinda Buhari ya faɗa a taron tattaunawa na gaggawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC

165
Shugaba Buhari a wajen taron tattaunawa na gaggawa na shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk wanda ya yi yunkurin sace akwatin zabe a yayin zabukan 2019 to a bakin ransa.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Litinin a wani taron gaggawa da ya yi da shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Sakatariyar Jam’iyyar dake Abuja.

Shugaba Buhari ya kara da cewa wadanda suke da halin sace akwati za su fahimci cewa a wannan karon shi ne abu na karshe na karya doka da za su iya yi.

“Duk wanda ya ce zai sace akwatinan zabe ko ya jagoranci ‘yan daba don kawo rikici, wannan ka iya zama keta doka na karshe da zai iya yi a rayuwarsa”, in ji Shugaba Buhari.

“Ba kasafai nake ba jami’an soji ko na ‘yan sanda iko su nuna rashin imani ba. Ba za a zarge mu ba, amma ba za mu yi magudin zabe ba. Ina so a mutunta ‘yan Najeriya, a bari su zabi duk wanda suke so a dukkan jam’iyyu. Ba na jin tsoron haka.

“Dukkan jihohi 36 na zagaya. Ina jin na samu cikakken goyon baya da zai iya kula da ni. Saboda haka, zan gargadi duk wanda yake tunanin yana da isasshen tasiri a yankinsa ya jagoranci wani gungun ‘yan daba su sace akwatina ko su tayar da hayaniya a wurin zabe, zai yi haka a bakin ransa”, a kalaman Shugaba Buhari.

A ranar 16 ga watan Fabrairu ne INEC ta dage manyan zabukan kasar, sa’o’i kadan kafin fara shi.
Hakan dai ya jawo ce-ce-ku-ce daga ‘yan Najeriya, musamman ‘yan siyasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan