INEC ta ɗauki matakin ƙarshe a rikicin APC na jihar Rivers

140
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce jam’iyyar APC a jihar Rivers ba za ta iya gabatar da ‘yan takara ba a zabukan wannan shekara.

Shugaban Hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya kawo karshen maganar lokacin da ya yi wa manema labarai jawabi ranar Laraba a Abuja gabanin zaben na ranar Asabar.

A cewarsa, Hukumar za ta yi biyayya ga hukuncin Kotun Koli wadda ita ce kotu mafi girma kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada.

“Game da maganar APC a jihar Rivers, ina jin Kotun Koli ta yanke hukunce-hukunce da dama game da batun kuma bisa wannan dalili, Hukumar Zabe ta yanke hukuncinta duba da hukuncin Kotun Koli.

“Kuma a Kundin Tsarin Mulkinmu, Kotun Koli ita ce waje na karshe da duk wani dan kasa zai iya kai kukansa. Kuma dole a samu karshen kara, kamar yadda lauyoyi ka iya cewa da zarar Kotun Koli ta yanke hukunci, dukkan hukumomi a Tarayyar Najeriya dole su yi biyayya ga hukuncin na Kotun Koli.

“Saboda haka, Hukumar Zabe a matsayinta na hukuma mai bin doka koyaushe za ta ci gaba da biyayya ga hukuncin kotuna, to haka ma abin yake a jihar Rivers. Babu kuma inda za a je. Za mu bi hukuncin dukkan kotuna, amma idan aka zo Kotun Koli, wannan karshen dukkan kararraki kenan”, in ji Mista Yakubu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan