Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce mutane 130 a kashe a kisan da aka yi a karamar hukumar Kajuru da ke jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne ga manema labarai bayan fitowarsu daga taron gaggawa da suka yi a kan tsaro tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja.
Gwamnan ya kara da cewa rahotannin da suka samu a baya-bayan nan sun tabbatar musu cewa mutum 130 aka kashe ba 66 ba kamar yadda aka fada.
Mista El-Rufa’i ya ce a matsayinsa na gwamna, ba ya aiki da jita-jita, sai an gudanar da bincike tare da tabbatar da gaskiyar lamari kafin ya bayyana shi, ya kuma ce yana aiki da dukkan jami’an tsaron dake jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahman ya ce zuwa yanzu sun kama mutum 11 da ake zargin suna da alaka da kisan, kuma suna ci gaba zurfafa bincike don bankado asirin wanda suka aikata kisan.
Taron na gaggawa da aka gudanar akan tsaro ya samu halartar gwamnonin Adamawa da Borno da Yobe da Kaduna.