Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Sokoto Muhammad Sadiq, ya ce jami’an ‘yan sanda sun kama wani mutum mai suna Shehu Maidamma dauke da takardun zabe na bogi.
Sadiq ya bayyana haka ne, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a garin Sokoto, inda ya ce sun kama Shehu dauke da wadannan takardu ne a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce hukumar zabe ta tabbatar masu cewa takardun da Shehu ke dauke da su na boge ne.
Haka kuma, bincike ya tabbatar wa rundunar cewa takardun jam’iyyar PDP se ta buga su, domin nuna wa masu zabe yadda za su zabe ta a ranar zabe.
Ya kuma bukaci mutane su kwantar da hankalin su, domin jami’an tsaro na aiki da hukumar zabe domin ganin zabe ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Jami’in hukumar zabe Muhammad Musa ya tabbatar da haka, inda ya ce takardun da aka kama Shehu da su ba ainihin takardun zabe ba ne, kuma jam’iyyu na da damar wayar da kan magoya bayan su game da yadda za su kada kuri’a.
Majiya: Liberty Radio