Hukumar INEC ta Bayyana Kuɗin da zata Biya Kowane Ma’aikacin zaɓe

212
Masu kaɗa ƙuri'a na bin layin zaɓe

Shugaban hukumar zaben Nijeriya Farfesa Muhamud Yakubu ya bayyana cewa N30,500 za a biya ma’aikatan wucin gadin da za su gudanar da babban zaben Nijeriya da za a fara gudanarwa a ranar Asabar mai zuwa 23 ga watan February 2019, da kuma na gwamnoni da yan majalissun jiha da za a gudanar a ranar 9 ga watan Mach.

Bayanin hakan ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da matasa masu yi wa kasa hidima suka fara kokawa a kan yadda aka dage zaben farko ba tare da an basu ko kudin abinci ba gashi kuma aka dage zaben har sun riga sun kai ga wuraren da za a gudanar da zaben da kudaden aljihunsu.
Da yake mayar da martani a kan koke-koken, Farfesa Muhamud Yakubu ya ce za a biya kudin tirenin da na abinci da zirgazirga gaba daya da suka kama naira N4,500, sai kuma kudin aikin zabe za su kama N13,000.

Tambarin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC

Ya ce kudin aikin zaben shugaban kasa dana yan majalissar tarayya da za a fara yi in an hada su gaba daya har da kudin tirenin za su kama N17,500 kenan.

Haka kuma shugaban hukumar INEC din ya ce zaben gwamnoni dana yan majalissar dokokin jihohi da za a yi a 9 ga watan Mach, da yake shi babu tirenin kudin aikin zaben za su koma naira dubu N13,000 daidai.

In ka hada kudin aikin zaben gaba daya za su kama naira dubu talatin da dari biyar N30,500 dai-dai kenan, inji shugaban INEC Muhamud Yakubu.

Turawa Abokai

3 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan