Umarnin nuna ba sani ba sabo ga ɓarayin akwatin zaɓe: PDP ta ba Burutai shawara

36
Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Janar Yusuf Tukur Burutai da sauran jami'an soji

Jam’yyar PDP ta shawarci Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Janar Yusuf Tukur Buratai da kada ya shigar da Rundunar Sojojin Kasar cikin harkokin siyasa.

Mista Kola Ologbondiyan, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar ne ya bada wannan shawara a jiya a Abuja.
Ya ce, Janar Buratai ya guji yin wasu kalamai ko ayyuka da zai nuna cewa Rundunar Sojojin Kasar nan goyon bayan wata jam’iyyar siyasa ko wani bangare.

Ya kara da cewa, Babbar Kotu dake zama a jihar Legas a ranar 23 ga watan Maris na shekarar 2015 da Kotun Daukaka Kara a ranar 15 ga watan Fabrairu sun tabbatar da cewa babu bukatar sojoji a lokacin gudanar da zabe, kuma kowane soja ya yi zabe a bariki.

Daga karshe ya yi kira ga Janar Buratai da ya maida hankali wajen sauke nauyin tsaron kasar nan da kawo karshen aikin ta’addanci.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan