Buhari ya doke Atiku da gagarumin rinjaye a jihar Gombe

0
Buhari da Atiku

Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya doke babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da gagarumin rinjaye a jihar Gombe a sakamakon zaben shugaban kasa da aka fitar a jihar.

Buhari ya samu kuri’u 402,961 a sakamakon kananan hukumomi 11 da Jami’in Tattara Sakamakon Zabe a jihar kuma Shugaban Jami’ar Fasaha ta Modibbo Adama dake Yola, Farfesa Kyari Mohammed ya sanar a hukumance.

Babban abokin hamayyar Shugaba Buhari, Atiku Abubakar ya samu kuri’u 138,484 a jihar.

Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa da wannan sakamako na karshe daga kananan hukumomi 11 dake jihar, Buhari ya samu kaso 73 cikin dari, inda Atiku ya samu kaso 25 cikin dari, yayinda sauran ‘yan takarar shugabancin kasa suka samu kaso biyu cikin dari.

Farfesa Kyari ya ce daga cikin masu kada kuri’a 1,385,191 da suke da rijista a jihar, an tantance 604,240 inda 580,649 suka kada kuri’unsu.

Ya ce daga cikin jimillar kuri’un da aka kada, kuri’u 554,203 su ne sahihai, yayinda aka yi watsi da kuri’u 26,446.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan