Dogara, Ekweremadu, Kabiru Gaya sun lashe zaɓe

236
Dogara a layin zaɓen

Kakakin Majalisar Dokokin Najeriya, Yakubu Dogara ya lashe zaben kujerar dan Majalisar Tarayya a jihar Bauchi.

Hukumar Zabe ta tabbatar da Mista Dogara a matsayin wanda ya lashe zaben dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balewa da Bogoro.

Misra Dogara, wanda ya yi takara a jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 73,609 inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Dalhatu Kantana, wanda ya samu kuri’u 50,078.

Hakan dai na nufin Mista Dogara, wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP zai dawo Majalisar Wakilai, kuma zai yi kokarin kare kujerarsa ta Kakakin Majalisar Wakilan, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Shi ma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, na jam’iyyar PDP ya sake lashe zaben Majalisar Dattawan Kudancin Enugu, kamar yadda BBC Hausa ta tabbatar.

Baturen Zaben yankin, Douglas Nwagbo ya ce Mista Ekweremadu ya samu kuri’a 86,088, yayin da abokiyar hamayyarsa ta jam’iyyar APC, Misis Juliet Ibekaku-Nwagwu ta samu kuri’a 15,187.

Wannan shi ne karo na biyar da Mista Ekweremadu yake lashe zabe a mazabar Sanata ta yankin.

BBC Hausa ta kara ruwaito cewa shi ma Sanatan dake wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, Kabiru Gaya, ya sake lashe zaben Majalisar a karkashin jam’iyyar APC.

Sanata Gaya ya samu kuri’a 319,004, yayin da abokan hamayarsa na PDP, Abdullahi Rogo ya samu kuri’a 217,520, sannan Yahaya Bala Karaye na jam’iyyar PRP ya samu kuri’a 30,013.

Baturen Zaben yankin, Farfesa Ibrahim Barde ne ya bayyana sakamakon zaben.

Wannan shi ne karo na hudu da Sanata Gaya zai wakilci yankin Kudancin Kano a Majalisar Dattawan Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan