Home / Gwamnati / Jawabin Shekarau Bayan Zaɓarsa Sanata

Jawabin Shekarau Bayan Zaɓarsa Sanata

Da sunan Allah Ta’ala, mai rahama da jinkai, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu SAW.

Ni Sanata Ibrahim Shekarau, mai wakiltar al’ummar jihar Kano Ta Tsakiya,, ina farawa da godiya ga Allah bisa wannan nasara da ya bamu ta cin zaben sanata a jam’iyyarmu ta APC.

Wannan nasara ta al’ummar mu ce gaba daya, don haka ina godiya garesu duka.
Ina amfani da wannan dama na godewa jama’ar Kano Central da suka ga dacewar su zabeni don na wakilcesu a majalisar dattijai ta Najeriya.

Malam Ibrahim Shekarau
Ina godiya matuka ga jam’iyyar APC ta kasa da ta jihar Kano da babban kwamitin kamfe dina da suka yi dawainiya har aka zo wannan matakin.

Haka kuma ina mika godiya ta musamman ga gwamnan jihar Kano da ‘yan majalisarsa da duk zababbunmu na APC masu komawa da sababbi da shugabanni zababbu na mulki da jam’iyya na Kano a kananan hukumomi.

Wannan nasara tamu ce gaba daya, kuma da yardar Allah, zamu ci gaba da amfani da ita don hidimtawa al’umma da basu wakilci na kwarai.

Nagode
Sanata Ibrahim Shekarau CON
Sardaunan Kano

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Rugujewar Kwankwasiyya ta kunno kai a jihar Kano – Fa’izu Alfindiki

Fitaccen mai adawa da tsarin siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kuma …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *