Da Sauran rina a Kaba: Atiku Abubakar Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓe

178

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai aminta ba da sakamakon babban zaɓen ƙasa da hukumar zaɓe ta bayyana ba.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, ya ƙara da cewa zaɓen cike ya ke da murɗiya gami da rashin gaskiya. Sabo da haka ba zai taɓa amincewa da sakamakon zaɓen ba.

A ƙarshe ya sha alwashin ƙalubalantar zaɓen a gaban kuliya, domin hakan ne kawai zai ceto tafarkin demokradiyyar ƙasar nan daga fuskantar barazana.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan