Rikicin Kajuru na baya-bayan nan: Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ya bayyana adadin mutanen da aka kama

165
Gwamna Nasir El-Rufa'i a Kajuru

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Ahmad Abdurrahman ya bayyana cewa an kashe mutane 29 a karamar hukumar Kajuru a jiya Talata.

Kwamishinan ya sanar da manema labarai a ofishinsa cewa harin da aka kai an kashe dan sanda daya tare da jiwa ‘yan sanda biyu ciwo tare da kona gidaje 40.

Mista Ahmad ya kara da cewa, DPO na karamar hukumar Kajuru ne ya kai masa rahoton harin wasu ‘yan bindiga a kauyen Karmai da Maro kuma kai-tsaye ya tura jami’an ‘yan sanda amma sai maharan suka far musu tare da bi gida-gida suna kone-kone da kashe-kashe.

Hakan ya sa Kwamishinan ya garzaya wurin da kan sa tare da karin jami’an tsaro inda suka shawo kan lamarin duk da cewa ba su samu nasarar cafke ‘yan bindigar ba.

Kwamishinan ya ce irin wannan kisan kiyashin ya isa haka, kuma hukuma ba za ta lamunta ba. Sannan ya yi kira ga mazauna garuruwan da su kasance masu aminci da juna domin zama cikin lumana.

A wani labari da jaridar Leardership ta wallafa a ranar Talata, al’ummar dake karamar hukumar Kajuru wanda rigingimu suka shafa sun nuna bukatarsu na komawa garuruwansu.

Kashe-kashen ya rutsa da rugogin Fulani da ‘yan kabilar Adara.

A wata hira da jaridar Leadership ta yi da shugaban Fulanin, Malam Lawal Adamu, ya ce su ba su san dalilin faruwar tashin hankalin ba, saboda shekara da shekaru, suna zaune lafiya da su da mutanen Adara, komai tare suka gudanarwa na harkar rayuwar yau da kullum. Har ta girke-girken bukukuwan Sallah da na Kirsimeti tare suke yi. Kuma ya ce, Fulani sun yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa Adara.

A nasa bangaren, Limamin Cocin Katolika ta Catholic ta St. Bernard Parish, Idon Gida, ya ce tsawon lokaci wata rigima ba ta taba shiga tsakanin su da Fulani ba, suna zaune lafiya da juna.

Shugaban jama’ar Kudancin Kaduna, Mista Solomon Musa ya dora alhakin rikicin dake faruwa akan gwamna Nasir El Rufa’i.

Ya zargi gwamnan da cewa duk bayan shekara hudu sai an samu rigima a Kudancin jihar ta Kaduna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan