Sheikh Gumi ya bayyana ra’ayinsa game da cin zaɓen Buhari

10
Sheikh Gumi

Babban Malamin addinin Musuluncin nan dake zaune a jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya soki nasarar da Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya samu a zaben Shugaban Kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairu na wannan shekara.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta bayyana sakamakon zaben a safiyar yau, 27 ga watan Fabrairu kuma Sheikh Gumi, ya koka bisa yadda Shugaba Buhari ya nuna tabbacin cin zaben sa tun kafin a bayyana sakamako.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito Sheikh Gumi yana cewa, “Tun kafin a kirga kuri’u, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi imani 100% cewa shi ne zai lashe zabe. Ta yaya ya san shi ne zai lashe zaben duba da cewa kan ‘yan kasar nan a rabe yake kuma ana fama da talauci da fatara?”

Malamin ya kara da cewa, gwamnatin Shugaba Buhari ba ta da ayyuka ko cancanta da za ta bugi kirji ta ce shi yasa aka zabe ta saboda tattalin arzikin kasa, da rashin tsaro da rashawa sun yi katutu, da karancin ayyukan yi, da karuwar kashe-kashe na kabilu, da karuwar sace mutane, da talauci ko wane lungu da sako.

Sheikh Gumi ya koka bisa yadda jam’iyyar APC ta dinga raba wa mata kudi domin su zabi APC, da amfani da yara wanda shekarunsu bai kai ba da kuma amfani da malamai wurin kamfen yayinda Shugaba Buhari ya yi amfani da EFCC wajen muzguna wa abokan hamayya, da razana masu zabe da sojoji, da amfani da kudin gwamnati wajen kamfen, da mamaye gidan radio da talabijin na gwamnati, da masallatai a kamfen da sauransu. Wannan shi ne halastacciyar rashawa.

A ta bakin Malamin, ta haka ne Shugaba Buhari ya samu tabbacin lashe zabe.
A karshe ya yaba wa dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar saboda jajircewarsa kuma ya yi kira ga al’umma su kasance masu bin doka.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan