Atiku ya mayar da martani mai zafi game da sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa

245
Buhari da Atiku

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce zaben da aka gudanar a shekara ta 2019 shi ne zabe mafi muni zabe da aka tabayi a kasar nan.

Atiku Abubakar ya fadi haka ne a jiya Laraba a Abuja yayin da yake zantawa da manema labarai.

Dan takarar ya nuna rashin jin dadinsa ga tsohon Shugaban Mulkin Soja na kasar nan, Janar Abdussalam Abubakar tare da ce masa ko a zamanin mulkin soja ba a taba yin zabe mai cike da abin kunya irin wannan ba.

“Kuma na gaya wa Janar Abdussalami Abubakar lokacin da ya kira cewa hatta zabukan da gwamnatocin soja suka gudanar ya fi shi inganci”, in ji Atiku.

Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su yi hakuri, ya ce kuma za su nemi hakkinsu a kotu duk da cewa zai dauki lokaci amma ya ba su tabbacin samun nasara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan