Hanyoyi 4 Da Zaki Gane Tsohon Masoyinki Na Sonki Har Yanzu

30

A lokuta da dama, mu kan tsinci kanmu a cikin yanayi na rabuwa da masoyi saboda wasu dalilai na rayuwa. Hakan yakan sa alaka a tsakanin masoya ya zo karshe.

Amma wani hanzari ba gudu ba anan shi ne, akan samu masoya da suke cigaba da son juna bayan rabuwa. Soyayyar zata cigaba da ginuwa a cikin ransu duk da cewa basa tare.

Wasu ma, sukan tsinci kansu a yanayi na cigaba da son masoyi ko masoyiya duk da cewa masoyansu tuni sun daina son su. Sai su dinga wasu dabi’u da ke nuna soyyayyansu ga tsofaffin masoyan nasu.

Ga hudu daga cikin hanyoyin da zamu iya gane soyayyar masoyi bayan rabuwa.

Masoyi kan nemi hanyoyi da za’a gina sabuwar alaka kamar ziyartar iyaye da yan uwa ko abokanan arziki ko kawaye.
Maida hankali da yiwa masoyi hidima ta hanyar bada lokaci ko kudi ko kaya ga tsohon masoyi.

Neman duk wata hanya da za’a samu wata saduwa kamar kira babu wani dalili, ko tura sakon text ko neman wani uzuri da zai sa a samu haduwa.

Nuna kishi akan tsohon masoyi. Kishi akan tsohon masoyi yana nuna cewa har yanzu akwai soyayya a cikin zuciyan mai kishi.

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan