‘Yan takarar jam’iyyun hamayya a jihar Kaduna za su mara wa El-Rufa’i baya

208
Gwamna El-Rufa'i

‘Yan takara 32 a karkashin tutar Kanduna State Progressive Governorship Candidate Forum sun amince su mara wa Gwamna Nasir El-Rufa’i na jam’iyyar APC baya a jihar Kaduna.

Sun amince da Gwamnan a matsayin dan takararsu a zaben gwamnoni da za a gudanar ranar Asabar.

A ranar Litinin ne suka sanar da hukuncin nasu lokacin da ‘yan takara 32 da jam’iyyau 49 suka amince da El-Rufa’i, suka tabbatar da shi a matsayin dan takararsu na maslaha.

Shugaban Jam’iyyar UDP na Jihar Kaduna, Kwamared Auwal Abdullahi Aliyu ya ce sun amince su mara wa Gwamnan baya ne don ya ci gaba da kyawawan ayyukansa, yana mai nanata cewa ya yi bajintar da ya kamata a mara masa baya.

“Mun dade muna tuntuba kuma daga karshe dai mun yanke hukunci. Saboda son jihar Kaduna, saboda ba za mu iya cin zabe ba, abinda muke da niyyar yi shi ne abinda yake yi tuni, saboda haka mun yanke shawarar mu mara masa baya.

“Ba kawunanmu muke kallo ba, muna kallon Kaduna ne da al’ummarta”, in ji Kwamared Aliyu.
Ya ce koda yake dai suna da manufofinsu da shirye-shirye, amma za su mara masa don ya yi nasara a Kaduna.

‘Yan takarar gwamnan sun hada da Auwal Aliyu na UDP; Matoh Yakubu na AGA; Umar Uba na NIP; Fatima Uba ta RP; Kabiru Idris na MPN; Ahmed Zagi na GPN; Mansur Suleiman na AA; Alhaji Yahaya Marafa na UPN; Abdulfatai Yusuf na WTPN, Umar Suleiman Abubakar na DA da Jubril Muhammed na ID.

Sauran sun hada da Mustapha Bakano na APA; Haliru Tafida na MRDD; Abubakar Aliyu na CAP; Abubakar Abdullahi na ZLP; Aminu Sabo na ANNP; Hajiya Rabiatu Suleiman Shula ta NAC; Kabiru Jibril na PPA; Adamu Idris Chado na DPC; Suleiman Abdulrasheed na MMN; Sani Mohammed Jamilu na Accord Party; Yahaya Solomon na NPC da sauransu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan