Yan Takarar Gwamnan Jihar Adamawa Goma sun Marawa Jam’iyyar PDP baya

172

Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP ya samu goyon bayan yan takarar gwamnan 10 daga jam’iyyu dabam dabam don samun nasara a zaben da za’a yi ranar asabar.

Kamfanin dillancin labarai ta kasa ce ta ce yan takarkarun sun yanke hukuncin marawa Alhaji Ummaru Fintiri baya ne a jiya litinin a garin Yola a wani taro da suka yi.

Yan takarkarun sunyi jawabi daya bayan daya kuma kowa ya bayyana dalilansa na marawa dan takarar jam’iyyar PDP baya a zaben da za’a yi.

Dan takarar jam’iyyar KOWA Bappari Umar yace, jam’iyyarsa ta mara jam’iyyar PDP baya ne a takarar gwamna kawai. A sauran matakai, zasu zabi yan takarkarun jam’iyyarsu.

A nata bangaren, yar takarar jam’iyyar CAP Elizabeth Isa, ta ce sun marawa Alhaji Ummaru Fintiri baya ne saboda shi mutum ne mai aiki da cikawa da hangen nesa. Hakan ya tabbata a locakin da ya rike mukamin shugaban majalisa na jiha.

Yan takarar guda goma sune: Sadiq Khaliel na jam’iyyar MRDD, da Danjuma Musa na jam’iyyar FJP, da Naziru Sa’ad na jam’iyyar ZLP, da Ahmad Hassan na jam’iyyar DA, da Salihu Danjuma na jam’iyyar APM, da Abdullahi Usman na jam’iyyar NCP, da Bappari Umar na jam’iyyar KOWA, da Lami Musa ta jam’iyyar PPN, da Elizabeth Isa na jam’iyyar CAP, da Frank Simone na jam’iyyar MEGA.

Daga karshe, Alhaji Ummaru Fintiri ya yaba musu bisa kokarin da suka yi tare da yi musu alkawari idan jam’iyyarsa ta lashe zabe to zai kafa gwamnati da zata hada kai da kowa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan