Abba Kabir Yusuf ne ɗan takarar PDP a Kano- INEC

56
Abba Kabir Yusuf

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce jam’iyyar PDP tana dan takarar gwamna a Kano.

A ranar Litinin ne wata Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a jihar Kano ta soke zaben fitar da gwanin da jam’iyyar PDPn Reshen Jihar Kano ta ce ta gudanar wanda ya ba Abba Kabir Yusuf nasarar zama dan takarar gwamna a jam’iyyar.

MA Magana da Yawun Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Aliyu Bello ya shaida wa BBC Hausa cewa hukuncin kotun game da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kano bai iso ga hukumar ba.

“Tuni akwai sunan jam’iyyar PDP a takardar zabe illa takaddama ce tsakanin ‘yan takarar jam’iyya kan wanda jam’iyya ta tsayar”.

“Takaddamar da ake ba wai ana maganar Jam’iyya ba ta tsaida dan takara ba ne, akwai sunan jam’iyya domin ta tsayar da dan takara,”, Mista Bello ya shaida wa BBC Hausa haka.

Ya ce idan INEC ta samu hukuncin dole za ta zauna ta yi nazari kafin ta bayyana matsayinta.

Da BBC ta tambaye shi ko yaya abin zai kasance idan har INEC ba ta samu hukuncin ba har ranar zabe? Sai ya ce: “za mu jinkirta mu saurara har sai mun tabbatar da abin da hukuncin ya kunsa”.

Dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Ibrahim Ali Amin-little ne ya shigar da karar, inda yake kalubalantar yadda aka yi zaben da har Abba ya zama dan takara.
Lauyoyin dake kare Abba Kabir Yusuf, wanda dan takarar Kwankwasiyy ne sun ce tuni suka daukaka kara, duk da sun yi ikirarin cewa hukuncin bai shafi Abba Kabir Yusuf ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan