Gaskiyar lamari game da korar Gwamnan CBN

251
Gwamman Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele

Shugaba Muhammadu Buhari bai kori Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ba, kamar yadda jaridar _TheCable_ da ake bugawa a Intanet ta tabbatar.

A jiya ne rahotanni suka bazu a kafafen sada zumunta na zamani da suke cewa Mista Emefiele ya karbi wasika daga Ofishin Shugaba Muhammadu Buhari dake bukatar ya ajiye aiki.

Amma wata majiya dake Fadar Shugaban Kasa ta ce babu gaskiya a rahotannin inda ta ce: “Shugaban Kasa ba shi da ikon korar Gwamnan CBN ba tare da amincewar Majalisar Dokoki ba. Rahotannin na bogi ne”.

Lokaci da jaridar The Cable ta danganta al’amarin da dakatar da Muhammad Sanusi II, sai majiyar ta ce: “Dakatarwa daban take da kora, kuma Emefiele bai yi wani abu na kuskure da zai sa a dakatar da shi ko a bukaci ya tafi hutu ba.”

Sashi na 8 na Dokar da ta Kafa CBN ta shekarar 2017 ta ce Shugaban Kasa zai iya cire Gwamnan CBN ne kadai “idan kaso biyu cikin uku na ‘yan Majalisar Dokoki ta Kasa sun amince da korar Gwamnan, wadanda za su bukaci lallai a cire shi”.

Ana sa ran wa’adin shugabancin Emefiele a matsayin Gwamnan CBN zai kare ne ranar 3 ga watan Yuni, 2019 lokacin da zai cika shekara biyar da nadawa.

Wata majiyar ta ce kusantowar cikar wa’adin mulkin nasa ne tasa jita-jitar ke yaduwa cikin sauri.

The Cable ta fahimci cewa Mista Emefiele ya je ofis ranar Litinin, kuma Ofishin Gwamnan bai karbi wata wasika mai kama da haka ba.

Za a iya sake nada Mista Emefiele a matsayin Gwamnan CBN matukar Shugaban Kasa ya gamsu kuma Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince.

Sashi na 10 na Dokar da ta Kafa CBN ta tanadi cewa: “Za a nada Gwamna da Mataimakin Gwamna a karon farko tsawon shekaru biyar, kuma kowane daga cikinsu zai iya cancanctar a sake nada shi na wani wa’adi da ba zai wuce shekara biyar ba”.

Dokar ba ta ce komai game da tafiya hutu ba, amma The Cable ta fahimci cewa Gwamnonin CBN ba sa tafiya hutu saboda hadarin aikinsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan