Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC, ta bayyanawa manema labarai cewa ta samu mafita ga matsalar da ta dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Kano.
Jami’in tattara bayanai na jihar Kano, Farfesa Bello Shehu ne ya bayyana hakan a yau litinin.
A daren jiya ne hatsaniya ta barke a karamar hukumar Nasarawa a yayin da ake tattara kuri’u wanda shine karamar hukumar da ta karshe don kuri’u su kammala a bayyana sakamakon zaben gwamna.
A lokacin hatsaniyar ne, aka yayyaga takardun da ke dauke da takardun da suke dauke da sakamakon kuri’un.
Yanzu haka, hukumar INEC tace, zata yi amfani da sakamakon da ke cikin na’urar tattara bayanai domin kara kirga kuri’un karamar hukumar Nasara saboda a samu a kammala tare da bayyana sakamakon
Turawa Abokai