Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana Gwamna Darius Ishaku na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Taraba.
Babban Jami’in Tattara Sakamakon Zabe na Jihar, Farfesa Shehu Iya na Jami’ar Moddibo Adama dake Adamawa ne ya bayyana sakamakon zaben a Ofishin INEC dake Jalingo a tsakar daren Litinin.
A cewar Farfesa Iya, Gwamana Ishaku na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 520,433 inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Danladi Hassan wanda ya samu kuri’a 362, 735.
Gwamna Ishaku ya samu nasarar lashe zaben ne a kananan hukumomi 11 da suka hada Yakum, Zinga, Yorro, Kai, Bali, Donga, Wukari, Bali, Gashaka, Kurmi da Ussa, yayinda babban abokin hamayyarsa, Danladi Hassan ya lashe zaben a kananan hukumomin Jalingo, Gassol, Ibbi da Karim Lami.
Da wannan nasara dai, jam’iyyar PDP ta shafe shekaru 20 kenan tana lashe zabe a jihar, tun daga shekarar 1999.
A bangare guda kuma, Gwamna Ishaku ya saka dokar ta baci a Jalingo, babban birnin jihar.
Hassan Mijimyawa, Babban Sakataren Yada Labaran Gwamna ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin. Sanarwar dai ba ta bayyana dalilin da yasa aka sa dokar ta bacin ba.
Dokar ta bacin ta togace ma’aikatan INEC da manyan wakilan jam’iyyu da masu sa ido.
Dokar za ta bada damar yin zirga-zirga ne daga 6 na safe zuwa 6 na yamma.