Kanawa za su dara: Gwamnatin Tarayya ta amince da sakin wasu maƙudan kuɗaɗe don inganta samar da ruwan sha a Kano

233
Taron tattaunawa na Majalisar Zartarwa ta Kasa

A ranar Laraba ne Majalisar Zartarwa ta Kasa, FEC ta amince da sakin Euro miliyan 64.7 don inganta samar da ruwan sha a jihar Kano.

Hajiya Zainab Ahmed, Ministar Kudi ce ta bayyana haka lokacin da take ganawa da manema labarai na Fadar Gwamnatin Tarayya ranar Laraba bayan taron tattaunawa na Majalisar Zartarwa ta Kasa da Shugaba Buhari ya jagoranta.

Ta ce aikin wanda Gwmantin Jihar Kano ce za ta aiwatar da shi zai inganta rayuwar al’ummar jihar.

“Yau a taron tattaunawa na Majalisar Zartarwa ta Kasa, mun samu amincewar sakin Euro miliyan 64, 750000 don Shirin Samar da Ruwan Sha na Kasa a Jihar Kano.

“Aikin zai inganta rayuwar mutane miliyan daya da rabi a cikin birnin Kano ta hanyar inganta yadda za a samu kyakkyawan ruwan sha, kuma muna bukatar a ƙara karfin kudi na Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Kano ta hanyar kara kudaden shugarta da inganta shugabancinta”, in ji Misis Ahmed.

A cewar Ministar, aikin zai yi wa kayan samar da ruwa kwaskwarima tare da gina wasu don inganta samar da ruwan sha ga al’ummar jihar Kano.

Ministar ta kara da cewa Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar Kano ce za ta gudanar da aikin ta hanyar Kwamitinta na Aiwatar da Aikace-aikacen Jiha.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan