
Jam’iyyar APC mai mulki ta nuna rashin jin dadinta bisa hukuncin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yanke na maimaita zabe a wasu jihohin kasarnan.
Jam’iyyar ta ce hukumar INEC taji kunya biyo bayan gazawarta wajen gudanar da sahihin zabe a kasarnan.
Kakakin jam’iyyar na kasa mista Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana hakan a jiya lahadi, 17 ga watan maris a lokacin da yake ganawa da manema labarai na kafar watsa labarai na Channels TV.
A yayin da yake gabatar da jawabi, mista Lanre ya ce yana da tabbacin cewa jam’iyyar sa ta APC zata samu nasarar lashe zabukan gwamnoni da basu kammala ba.Sannan yayi kira ga hukumar INEC da ta gudanar da zabe na gaskiya kuma tsarkakakke.
Kamar yadda rahotonni suka nuna a baya, jam’iyyar APC na zargin jam’iyyar PDP da yin magudi a zabukan kasa don samun rinjaye. Hakan yasa suke aikata duk wani nau’i na rashin gaskiya kama daga tada hankali a lokacin zabe, zuwa sayen kuri’u, da sauran ayyuka na batanci wanda hakan na daga cikin dalilan da suka sa aka dage zaben shugaban kasa a wancan lokaci.