INEC ta ɗage zaɓe a ɗaya daga cikin jihohin da za a sake zaɓen gwamna

113


Ba za a sake zaɓen gwamna a jihar Adamawa ba a gobe Asabar sakamakon ƙara da jam’iyyar MRDD ta shigar a Babban Kotun Jihar.

Jam’iyyar MRDD ta shigar da ƙarar ne bisa ƙorafin cewa ba a sa alamarta ba a zaɓen gwamna na ranar 9 ga watan Maris da aka bayyana a matsayin wanda bai kammala ba.


Bayan sauraren bahasi daga wadda ake ƙara, wato INEC da mai shigar da ƙara wato MRDD, Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Abdulaziz Waziri ya ɗage zaman Kotun zuwa ranar Talata, 26 ga watan Maris, ya kuma ƙara tsawon wa’adin hanin da aka yi wa INEC na ci gaba da gudanar da zaɓen gwamna a jihar.


Amma Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar, Barrista Tahir Shehu ya ce duba da hukuncin kotun, INEC za ta iya jinkirta zaɓen gwamnan ne kawai, ba wai ta soke zaɓen gwamnan gaba ɗaya ba.


Ya ce ya yi imani cewa bayan hukuncin kotun na ranar Talata, INEC za ta sake sabuwar ranar da za a gudanar da zaɓen.
Daga nan Mista Shehu ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar da su kwantar da hankalinsu su kuma jira sakamakon hukuncin kotun.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan