Zaɓen gwamnan Kano: ‘Yan Sanda sun cafke Kwamishinan Ganduje bisa zargin sa da yunƙurin tada tarzoma

140


A ranar Asabar ne jami’an ‘yan sanda suka cafke Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, Muktar Ishaq Yakasai wanda ake zargin ya jagoranci wasu gungun ‘yan daba zuwa Makarantar Sakandare dake Yelwa don tayar da hankulan masu zaɓe.


Jaridar Solacebase ta gano cewa zaɓen gwamnan da ake sakewa a jihar Kano a yau ya ci karo da tada hankali da raunata mutane.


Yunƙurin ji daga Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi bai yi nasara ba don kuwa bai ɗauki wayar da aka yi masa ba.


Amma wakilin jaridar Solacebase ya bada rahoton cewa jami’an ‘yan sanda sun yi awon gaba da Muktar Ishaq tare da waɗanda aka kama su.


An hana gidan Talabijin na TVC aiwatar da aikinsu a Gama, yayinda su ma BBC ba a ƙyale su ba.


Akwai rashin tsaro a jihar Kano ƙarara yadda za a iya ganin yadda ‘yan dabar siyasa ke iko da wuraren kaɗa ƙuri’a.


Wakilan Solacebase sun ga yadda aka kai wa magoya bayan wata jam’iyya hari a ƙananan hukumomin Rimin Gado, Dala, Kibiya da Tudun Wada.

A cewar BBC, masu kaɗa ƙuri’a baƙi fiye da 25000 suke mamaye unguwar Gama dake ƙaramar hukumar Nasarawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan