A jiya alhamis, 28 ga watan maris, kasar Chadi ta cika shekara guda da katse kafofin sadarwa bayan gudanar da taron kasa wanda ya yi tanadin gyaran kundin tsarin mulki da zai ba shugaban kasar damar cigaba da mulki har zuwa shekarar 2033.
BBC Hausa sun rawaito cewa shugaban Kasa Idriss Deby ya fitar da doka da ta hana amfani da kafofin sadarwa a kasar biyo bayan amfani da ake da shafukan sada zumunta don shirya zanga-zangar kin jinin gwamnatin sa.
Wakilin BBC Vincent Ndjamena ya bayyana cewa masu sukar gwamnatin shugaba Deby sun yi ta shirya zanga-zangar kin jinin gwamnati ta shafukan sada zumunta kuma hakan ya zama barazana ga gwamnati a wannan lokaci. Hakan yasa gwamnati ta toshe damar shiga Facebook, da Twitter da WhatsApp, matakin da ya taimaka wajen rage yawan zanga-zangar.
Deuh’b Emmanuel, mai rubuce rubuce a kafar Internet ya shaida wa BBC cewa “rashin damar shiga shafukan sada zumunta kamar zama a gidan yari ne ba tare da gidan yarin ba”.
A jiya laraba 28 ga watan maris, mai magana da yawun gwamnati Oumar Yaya Hissein ya shaidawa BBC cewa gwamnati ta katse kafofin sadarwan saboda tsaro.
Gwamnatin Chadi ta bukaci taimakon sojojin kasar Faransa kuma a watan Fabrairun na wannan shekarar, sojojin na faransa suka kai hari akan jerin motocin yan adawa da ke dawowa daga kasar Libya dauke da makamai.
Wasu rukunin lauyoyi na ta fafutuka akotu don ganin gwamnati ta dawo da damar shiga shafukan sada zumunta amma har yanzu haķansu bai cimma ruwa ba, domin kuwa sun kasa samun nasara a kotu.
Duk da haka, wasu lauyoyi karkashin jagorancin Daïnoné Frédéric da Frédéric Nanadjingué sun sha alwashin ķalubalantar toshewar ta hanyar jawo hankalin kasashen duniya.
Shugaba Idriss Deby ya bari mulki a kasar Chadi tun a shekarar 1990. Yanzu haka ya shafe shekaru 29 yana kan karagar Mulki.