Majalisar Dinkin Duniya: Dokar Kasar Brunei Koma Baya Ne Ga Yancin Dan Adam

40

Majalisar Dinkin Duniya (United Nation) ta yi Allah wadai ga tatstsauran matakin da kasar Brunei ta dauka. Sabon dokar da kasar ta kafa ana sa ran zai fara aiki ranar laraba mai zuwa.

Shugaban kungiyar kare Yancin dan Adam karkashin majalisar, Michelle Bachelet ce ta bayyana hakan, inda ta ce dole su nuna damuwa matuka akan hukuncin zalunci, da wulakanci da cin zarafin zarafin mutane da ke kunshi a cikin sabon dokar.

Sabon dokar na kasar Brunei ya kunshi hukunce-hukunce kisa ta hanyar jefewa ga wanda aka kama da laifukan aikata Luwadi, da Madigo, da Zina, da Fashi da makami, da Zagin ko aibata Manzon Allah (SAW). Sai hukuncin yanke hannu ga wanda yayi sata, sai bulala ga wanda aka kama da laifin zubar da ciki. Sannan kuma laifi ne babba idab aka kama mutum yana koyar da yara musulmi wani abu da ya danganci wani addinin da ba musulunci ba.

Maganar shugaba Bachalet ya yi dai-dai da kiraye kirayen yan siyasa da fitattun mutane akan sabon dokar kuma sun ba da shawaran kauracewa cinikayya da gwamnatin na Brunei don nuna fushin su.

Kasar Brunei kasaa ce da ta ke makotaka da kasasken Malaysia da Indonesia kuma dukkanin su kasashe ne na musulmai. Amma ita kasar ta Brunei ta fi makotanta yin amfani da dokoki masu tsauri na Musulunci.

Kasar tana amfani da tsarin sarauta, a yanzu haka, Sultan Hassanal Bolkiah ne ke mulkin kasar. Ya shafe kimanin shekaru 51 yana mulku.

Shugabar ta kara da cewa wannan sabon dokan zai iya haifar da rigingimu, da tsangwama ga wasu jinsi a kasar. Don haka ta ke kira ga shugabanni a kasar da su sassauta saboda tabbatar da dokar zai kawo koma baya ga yancin dan Adam a duniya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan