Abubuwan da suka faru lokacin da INEC ta ba Ganduje Takardar Shaidar Cin Zaɓe

152

A ranar Laraba ne Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta, Ƙasa INEC ta ba Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje Takardar Shaidar Cin Zaɓe.


Haka kuma, Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna tare da wasu ‘yan Majalisun Dokokin Jihar 23 su ma sun karɓi Takardu Shaidar Cin Zaɓen.


Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya bada rahoton cewa ba a ga ‘yan Majalisun Dokokin Jihar Kano 13 da aka zaɓa a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP ba yayin bikin bada Takardun Shaidar Cin Zaɓen wanda aka gudanar a Rufaffen Ɗakin Wasa na Sani Abacha dake Jihar.


Da yake jawabi jim kaɗan bayan ya karɓi Takardar Shaidar Cin Zaɓen, Gwamana Ganduje ya yi alƙawarin shimfiɗa kadarkon ci gaba mai ƙwari don inganta walwalar al’ummar jihar Kano.


A cewarsa, nan ba da daɗewa ba Gwamnatin Jihar za ta bayyana shirye-shiryenta don jawo hankalin masu zuba jari na gida da waje don su zo jihar Kano su zuba jari.


Ya ce Gwamnatin Jihar za ta samar da kyakkyawan yanayi ga masu sha’awar zuba jari a jihar don su samu yin hakan cikin sauƙi.


“Duk wanda yake so ya kafa kasuwanci ko cibiyar ilimi, Kano tana yi masa/mata maraba.


“Dole mu tabbatar da cewa dukkan ‘ya’yanmu mata sun samu ilimi mai nagarta. Dole kuma mu tabbatar da cewa dukkan ‘ya’yanmu mata sun samu ilimi, ta yin hak za mu iya buɗe kaso 50 cikin ɗari na ci gaban tattalin arziƙi da ba ma iya buɗewa saboda rashin shigar mata.


“Dole kuma mu tabbatar da cewa jiharmu ta zama waje mai ban sha’awa da za a iya zuba jari da kasuwanci, tare da mayar da hankali ga zuba jari da zai bunƙasa rayuwar al’ummarmu”, in ji Gwamna Ganduje.


Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba Gwamnatin Jihar haɗin kan da take buƙata don ciyar da jihar gaba.


Da yake jawabi tun da farko, Kwamishinan INEC a Jihar Kano, Farfesa Riskuwa Arab Shehu ya ce Hukumar za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin da suka dace kan batun wayar da kan masu zaɓe.


Shi ma da yake jawabi, Kwamishinan INEC na Ƙasa mai kula da jihohin Kano, Katsina da Jigawa, Mista Abubakar Nahuce, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su yi ruƙo da ɗabi’ar ƙwarai don samu ci gaba a ƙasa gaba ɗaya.


NAN ya bada rahoton cewa zaɓaɓɓun ‘yan Majalisun Dokokin Jihar da aka zaɓa a jam’iyyar PDP waɗanda ba su halarci bikin bada Takardun Shaidar Cin Zaɓen ba sun haɗa da na ƙaramar hukumar Dala, Nasarawa, Kano Municipal, Gwale, Fagge da Tarauni.


Sauran su ne na Kibiya, Kumbotso, Dawakin Kudu, Gezawa, Ungogo, Bebeji da Rogo.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan