INEC ta bayyana sakamakon zaɓen gwamna a Rivers

65

A ranar Laraba ne Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta bayyana Gwamna Nyesom Wike, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar ranar 9 ga watan Maris a jihar.

Jami’in Tattara Sakamakon Zaɓen Gwamanan Jihar, Teddy Adias, wanda kuma a lokaci guda shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Otuke, Jihar Bayelsa ya bayyana Gwamna Wike a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar dake cike da rikici a birnin Port Harcourt.

Gwamna Wike ya samu kuri’a 886,263 inda ya doke Mista Biokpomaba Awara na jam’iyyar AAC wanda ya samu kuri’a 173,859.

“Cewa Nyesom Wike na jam’iyyar PDP, sakamakon cika ƙa’idojin doka, da kuma samun ƙur’u mafi yawa, an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, kuma ya tabbata zaɓaɓɓe”, in Farfesa Adias.

Farfesa Adias ya ce akwai ratar ƙuri’a 712,405 tsakanin Gwamna Wike da Mista Awara.

Ya ce adadin waɗanda suka yi rijistar zaɓe a jihar ya kai 3,048,741, jimillar waɗanda aka tantance ya kai 1,130, 445, jimillar ƙuri’u da aka kaɗa sun kai 1,123,840, jimillar sahihun kuri’u sun kai 1,102,823, yayin da jimillar ƙuri’un da suka lalace ya kai 249,324.

Mista Chukwunenye Kocha, wakilin jam’iyyar AAC ya ce jam’iyyar za ta yi nazarin sakamakon zaɓen kafin ta ɗauki wani mataki.

Amma Mista Kocha ya ce jam’iyyar tana son zaman lafiya. Ya roƙi al’ummar jihar Rivers da sauran jam’iyyun siyasa da su ci gaba da zama lafiya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan